Buhari zai gabatar da kasafin kudin 2019


 Aika wannan shafi Email Aika wannan shafi Facebook Aika wannan shafi Twitter Aika wannan shafi Whatsapp
Image copyright GETTY IMAGES Kasafin kudi
Ranar Laraba ake sa ran shugaban Najeriya Muhammadu zai gabatar da kasafin kudin shekarar 2019 ga 'yan majalisar dokokin kasar.

Shugaban na Najeriya zai gabatar da kasafin kudin ne kasa da wata bakwai bayan ya sanya hannu a kasafin kudin shekarar 2018.

Wani dan majalisar dattawan kasar, Sanata Kabiru Gaya, ya shaida wa BBC cewa suna sa ran kasafin da shugaban zai gabatar zai zarta na 2018, wato N9.12 tr.

Kasafin kudi: Ban ji dadin cushen da majalisa ta yi ba - Buhari
Buhari ya kammala tsara kasafin kudin 2018
A cewarsa, gwamnatin kasar ta aiwatar da fiye da rabi na kasafin kudin da ya gabata, musamman a fannin ayyuka.

An sha kai ruwa rana tsakanin 'yan majalisar dokokin da shugaban kasa game da kasafin kudin shekarun da suka gabata.

Shugaba Buhari ya dade yana zargin 'yan majalisar da sanya ayyuka na son rai a kasafin kudin da yake gabatar musu, ko da yake su ma sun ce aikinsu ne tsefe kundin kasafin domin ganin an yi wa kowanne bangare na kasar adalci.

Wannan dai shi ne kasafin kudi na karshe da Shugaba Buhari zai gabatar wa 'yan majalisar gabanin babban zaben kasar da za a yi a watan Fabrairu.

Comments

Popular posts from this blog

GENERAL OVERSIGHT OF DEVELOPMENTAL PROJECTS BY OUR HON. MEMBER (HON. SALISU IRO ISANSI) MEMBER REPRESENTING KATSANA LOCAL GOVERNMENT FEDERAL CONSTITUENCY.

MAFI CANCANTA DA YABAWA ACIKIN YAN MAJALISSU HON. DANLAMI KURFI DOMIN YAYI KYAKKYAWAN TALLAFI WANDA ZAI INGANTA LAFIYAR AL UMMAR YANKINSA TA HANYAR RABA MASU MAGUNGUNA KYAUTA NA TSABAR KUDI HAR NAIRA 5,668,122.10

KATSINA GOVT SET TO ESTABLISHED UMYUK AGRIC FACULTY IN MALUMFASHI.