Posts

Showing posts from December, 2018

Buhari zai gabatar da kasafin kudin 2019

Image
  Aika wannan shafi Email Aika wannan shafi Facebook Aika wannan shafi Twitter Aika wannan shafi Whatsapp Image copyright GETTY IMAGES Kasafin kudi Ranar Laraba ake sa ran shugaban Najeriya Muhammadu zai gabatar da kasafin kudin shekarar 2019 ga 'yan majalisar dokokin kasar. Shugaban na Najeriya zai gabatar da kasafin kudin ne kasa da wata bakwai bayan ya sanya hannu a kasafin kudin shekarar 2018. Wani dan majalisar dattawan kasar, Sanata Kabiru Gaya, ya shaida wa BBC cewa suna sa ran kasafin da shugaban zai gabatar zai zarta na 2018, wato N9.12 tr. Kasafin kudi: Ban ji dadin cushen da majalisa ta yi ba - Buhari Buhari ya kammala tsara kasafin kudin 2018 A cewarsa, gwamnatin kasar ta aiwatar da fiye da rabi na kasafin kudin da ya gabata, musamman a fannin ayyuka. An sha kai ruwa rana tsakanin 'yan majalisar dokokin da shugaban kasa game da kasafin kudin shekarun da suka gabata. Shugaba Buhari ya dade yana zargin 'yan majalisar da sanya ayyuka na son rai a k