Abubuwa 10 Da Masari Ya Yi Wa Harkar Ruwa Da Aka Kasa Yi Cikin Shekaru 30 1st February 2018 Katsina Media and Publicity El Zaharadeen Umar Kungiyar tsofafin ma’aikatan ruwa na jihar Katsina sun bayyana gamsuwarsu da irin kamun ludayin gwamnatin Aminu Bello Masari dangane da yadda ta maida hankali wajen kokarin samar da ruwan sha a jihar Katsina. Shugaban kungiyar a jihar Katsina Alhaji Isah Abubakar Matazu ya bayyana haka lokacin da suka kira taron manema labarai a Katsina inda suka nuna jin dadinsu musamman irin ayyukan da suka ce gwamnatin Masari ta yi a bangaran ruwan sha. Ya kara da cewa wannan kungiya ta su an kafa ta ne domin ta bada gudunmawa wajen ganin an samu nasarar da ake bukata musamman akan sha’anin samar da ruwan sha a jihar Katsina wanda ya zama wani kalubale a cikin shekaru fiye da talatin da kirkira jihar Katsina. Alhaji Isah Abubakar ya bayyana cewa lokacin da suka yi wani taro a jihar Kwara ashekarar 2017 an bayyana hukumar samar da ruwa ta RUWASSA da ke Katsina ta zo na daya wajen samar da tsaftattcen ruwan sha a fadin tarayyar Najeriya. Daga nan ya cigaba da bayyana wasu nasarori goma da ya ce an samu karkashin wannan gwamnatin a cikin shekaru biyu da rabi da suka hada da kafa wani kwamnitin da ya bada cikakken rahoto game da halin da wuraran samar da tsaftattacen ruwa sha suke a jihar, wanda zai bada damar magance matsalar cikin sauki. Abu na biyu cewarsa shi ne, kafin zuwan wannan gwamnati an yi watsi da madatsar ruwa ta Malumfashi kusan fiye da shekaru bakwai inda ruwa ya yi kaca-kaca da kayayyakin aikin, amma gwamna Masari ya bada aikin gyaran wannan Dam da ofisosh da gidajen ma’aikata da hanya domin samun sauki zirga-zirga. Ya kuma bayyana cewa gwamna Masari ya bada gyaran gina madatsun ruwa sabbi a Kafur da Masari domin samar da ruwa sannan ya bayar da aikin kewaye madatsar ruwa ta Zangon Daura wanda zai yi amfani da hasken rana wannan yanki. Shugaban kungiyar tsofafin ma’aikatan ruwan ya bayyana cewa wannan gwamnatin ta kammala aikin madatsar ruwan ta Dandume da ta lalace shekara da shekaru, haka kuma an bada aikin gyaran ma’aitakar ruwa ta garin Funtua tare da sanya sabbin kayayyakin aiki na zamani. Sauran nasarorin da kungiyar ta ce an samu a karkashin gwamnatin Masari ta bangaran ruwa sha sun hada da daukaka darajar samar da ruwa ta hanyar kara inganta madatsun ruwa guda shida a garin Katsina domin samar da wadataccen ruwa a cikin birnin Katsina. Kazalika kungiyar ta yi ikirarin cewa gwamna Masari ya yi nasarar hada kai da gwamnatin tarayya wajen ganin an fara aikin da madatsar ruwa ta zobe da ta kai shekaru talatin, amma yanzu zata fara aikin samar da ruwa a wasu garuruwan da suke da makwabtaka da garin Dutsinma. Nasara ta goma da shugaban kungiyar ya ce abu ne da ba za a taba mantawa da shi ba shi ne, yadda wannan gwamnatin ta kudiri aniyar daukaka darajar madatsun ruwa na Daura da Katsina da Dutsinma da kuma Funtua wanda yanzu haka ana kan aikinsu. Daga karshen shugaban kungiyar ya ce a matsayinsu na tsofafin ma’aikatun ruwa gwamna Masari ya nuna masa tare inda ya biya su hakokkinsu da suka dade ba a biyasu ba, inda ya ce a karon farko an biya su kudi, naira miliyan 124, 744.133 sannan aka sake biyansu naira miliyan 20,401,725 saboda haka suna kara nuna godiyarsu tare da yin alkawarin cigaba da bada goyan baya ga gwamnatin Aminu Bello Masari musammana akan sha’anin ruwan sha a jihar Katsina. El Zaharadeen Umar katsina .

Kungiyar tsofafin ma’aikatan
ruwa na jihar Katsina sun bayyana gamsuwarsu da irin kamun
ludayin gwamnatin Aminu Bello Masari dangane da yadda ta
maida hankali wajen kokarin samar da ruwan sha a jihar
Katsina. Shugaban kungiyar a jihar Katsina Alhaji Isah
Abubakar Matazu ya bayyana haka lokacin da suka kira taron
manema labarai a Katsina inda suka nuna jin dadinsu
musamman irin ayyukan da suka ce gwamnatin Masari ta yi a
bangaran ruwan sha. Ya kara da cewa wannan kungiya ta su an
kafa ta ne domin ta bada gudunmawa wajen ganin an samu
nasarar da ake bukata musamman akan sha’anin samar da
ruwan sha a jihar Katsina wanda ya zama wani kalubale a cikin
shekaru fiye da talatin da kirkira jihar Katsina. Alhaji Isah
Abubakar ya bayyana cewa lokacin da suka yi wani taro a jihar
Kwara ashekarar 2017 an bayyana hukumar samar da ruwa ta
RUWASSA da ke Katsina ta zo na daya wajen samar da
tsaftattcen ruwan sha a fadin tarayyar Najeriya. Daga nan ya
cigaba da bayyana wasu nasarori goma da ya ce an samu
karkashin wannan gwamnatin a cikin shekaru biyu da rabi da
suka hada da kafa wani kwamnitin da ya bada cikakken rahoto
game da halin da wuraran samar da tsaftattacen ruwa sha
suke a jihar, wanda zai bada damar magance matsalar cikin
sauki. Abu na biyu cewarsa shi ne, kafin zuwan wannan
gwamnati an yi watsi da madatsar ruwa ta Malumfashi kusan
fiye da shekaru bakwai inda ruwa ya yi kaca-kaca da
kayayyakin aikin, amma gwamna Masari ya bada aikin gyaran
wannan Dam da ofisosh da gidajen ma’aikata da hanya domin
samun sauki zirga-zirga. Ya kuma bayyana cewa gwamna
Masari ya bada gyaran gina madatsun ruwa sabbi a Kafur da
Masari domin samar da ruwa sannan ya bayar da aikin kewaye
madatsar ruwa ta Zangon Daura wanda zai yi amfani da
hasken rana wannan yanki. Shugaban kungiyar tsofafin
ma’aikatan ruwan ya bayyana cewa wannan gwamnatin ta
kammala aikin madatsar ruwan ta Dandume da ta lalace
shekara da shekaru, haka kuma an bada aikin gyaran
ma’aitakar ruwa ta garin Funtua tare da sanya sabbin
kayayyakin aiki na zamani. Sauran nasarorin da kungiyar ta ce
an samu a karkashin gwamnatin Masari ta bangaran ruwa sha
sun hada da daukaka darajar samar da ruwa ta hanyar kara
inganta madatsun ruwa guda shida a garin Katsina domin
samar da wadataccen ruwa a cikin birnin Katsina. Kazalika
kungiyar ta yi ikirarin cewa gwamna Masari ya yi nasarar hada
kai da gwamnatin tarayya wajen ganin an fara aikin da
madatsar ruwa ta zobe da ta kai shekaru talatin, amma yanzu
zata fara aikin samar da ruwa a wasu garuruwan da suke da
makwabtaka da garin Dutsinma. Nasara ta goma da shugaban
kungiyar ya ce abu ne da ba za a taba mantawa da shi ba shi
ne, yadda wannan gwamnatin ta kudiri aniyar daukaka darajar
madatsun ruwa na Daura da Katsina da Dutsinma da kuma
Funtua wanda yanzu haka ana kan aikinsu. Daga karshen
shugaban kungiyar ya ce a matsayinsu na tsofafin ma’aikatun
ruwa gwamna Masari ya nuna masa tare inda ya biya su
hakokkinsu da suka dade ba a biyasu ba, inda ya ce a karon
farko an biya su kudi, naira miliyan 124, 744.133 sannan aka
sake biyansu naira miliyan 20,401,725 saboda haka suna kara
nuna godiyarsu tare da yin alkawarin cigaba da bada goyan
baya ga gwamnatin Aminu Bello Masari musammana akan
sha’anin ruwan sha a jihar Katsina. El Zaharadeen Umar

Comments

Popular posts from this blog

GENERAL OVERSIGHT OF DEVELOPMENTAL PROJECTS BY OUR HON. MEMBER (HON. SALISU IRO ISANSI) MEMBER REPRESENTING KATSANA LOCAL GOVERNMENT FEDERAL CONSTITUENCY.

MAFI CANCANTA DA YABAWA ACIKIN YAN MAJALISSU HON. DANLAMI KURFI DOMIN YAYI KYAKKYAWAN TALLAFI WANDA ZAI INGANTA LAFIYAR AL UMMAR YANKINSA TA HANYAR RABA MASU MAGUNGUNA KYAUTA NA TSABAR KUDI HAR NAIRA 5,668,122.10

KATSINA GOVT SET TO ESTABLISHED UMYUK AGRIC FACULTY IN MALUMFASHI.